Sojojin Syria Sun Isa kilo mita 16 da iyakar Kasar Turkiya.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i406-sojojin_syria_sun_isa_kilo_mita_16_da_iyakar_kasar_turkiya.
Sojojin Kasar Syria sun karaci garin Tal-Rif'ata mai nisan kilo mita 16 kacal daga iyakar kasar Turkiya.
(last modified 2018-08-22T06:57:46+00:00 )
Feb 07, 2016 02:17 UTC
  • Sojojin Syria Sun Isa kilo mita 16 da iyakar Kasar Turkiya.

Sojojin Kasar Syria sun karaci garin Tal-Rif'ata mai nisan kilo mita 16 kacal daga iyakar kasar Turkiya.

Tashar Telbijin din almayadden mai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta ambaci cewa; A halin da ake ciki a yanzu, sojojin na Syria da su ka kwace garuruwan Mayer da Ratyan, a arewacin gundumar Halab, sun nufi garin Tal-Rif'at, wanda nisansa daga "Babus-Salam' na iyakar Turkiya, bai wuce kilo mita 16 ba."

Garin Mayer ne dai cibiya mai muhimmanci da 'yan ta'addar kungiyar al-Nusrah, su ka yi tunga a cikin gundumar Halab. Tuni dai sojojin kasar ta Syria su ka kwace garin bayan kashe 'yan ta'adda 120.

A cikin watannin bayan nan dai sojojin Syria suna samun galaba akan 'yan ta'adda da Saudiyya da Turkiya su ke goyawa baya.