Dakarun Iraki Na Kara Fadada Farmakinsu Domin Kwato Mausul Daga ISIS
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4096-dakarun_iraki_na_kara_fadada_farmakinsu_domin_kwato_mausul_daga_isis
Dakarun gwamnatin kasar Iraki suna ci gaba da nausawa a cikin yanknan lardin nainawa da ke hannun 'yan ta'addan ISIS, da nufin kwace Mausul babban birnin Lardin, kma babbar cibiyar 'yan ta'addan ISIS a kasar Iraki a halin yanzu.
(last modified 2018-08-22T06:58:09+00:00 )
Apr 19, 2016 10:46 UTC
  • Dakarun Iraki Na Kara Fadada Farmakinsu Domin Kwato Mausul Daga ISIS

Dakarun gwamnatin kasar Iraki suna ci gaba da nausawa a cikin yanknan lardin nainawa da ke hannun 'yan ta'addan ISIS, da nufin kwace Mausul babban birnin Lardin, kma babbar cibiyar 'yan ta'addan ISIS a kasar Iraki a halin yanzu.

A cikin wani bayani wanda rundunar sojin kasar Iraki ta bayar a yau an bayyana cewa, dubban dakarun kasar sun kwace wasu kauyuka da ke kusa da birnin Mausul daga jiya Litin zuwa yau Talata, bayan halaka adadi mai yawa na mayakan 'yan ta'addan ISIS.

Tuna cikin watan Maris da ya gabata ne dai dakarun kasar ta Iraki suka sanar da fara kaddamar da farmakin kwato Mausul, wannan yunkuri na dakarun Iraki ya kada wa hantar wasu daga cikin sarakunan larabawa da ke da hannun wajen daukar nauyin 'yan ta'addan na Daesh (ISIS)

Bayanin rundunar sojin Iraki ya kara da cewa wannan shiri yana tafiya cikin nasar, kumada yardar ubangiji ana sa ran kammala murkushe 'yan ta'addan kasa da lokacin da aka diba musu.