MDD: Kimanin Mutane 400,000 Ne Suka Mutu A Rikicin Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4261-mdd_kimanin_mutane_400_000_ne_suka_mutu_a_rikicin_siriya
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar kimanin mutane 400,000 ne suka rasa rayukansu a kasar Siriya tsawon shekaru biyar na yakin basasan da ke faruwa a kasar sakamakon ci gaba da goyon bayan da wasu kasashen larabawa suke ba wa 'yan ta'addan da suka shigo da su kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:10+00:00 )
Apr 23, 2016 06:35 UTC
  • MDD: Kimanin Mutane 400,000 Ne Suka Mutu A Rikicin Siriya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar kimanin mutane 400,000 ne suka rasa rayukansu a kasar Siriya tsawon shekaru biyar na yakin basasan da ke faruwa a kasar sakamakon ci gaba da goyon bayan da wasu kasashen larabawa suke ba wa 'yan ta'addan da suka shigo da su kasar.

Manzon Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan kasar Siriyan Staffan de Mistura ne ya bayyana hakan a jawabin da yayi a bayan fagen taron sulhun kasar Siriyan da ke gudanar a birnin Geneva na kasar Swiss inda ya ce a bisa binciken da ya gudanar adadin mutanen da suka rasa rayukan na su tsawon wadannan shekaru biyar na yakin sun kai mutane dubu 400.

Wannan adadi na MDDn dai yayi kusa da wasu cibiyoyin ciki kuwa har da cibiyar nan ta Syrian Center for Policy Research ta fitar inda ta ce kimanin mutane dubu 470 ne suka rasa rayukan na su.

A watan Maris na shekara ta 2011 ne dai rikicin kasar Siriyan ya barke inda kasashe irin su Saudiyya, Turkiyya da Qatar suka kasance a sahun gaba cikin kasashen da suka dinga taimakon 'yan ta'addan da suka shigo da su Siriya da kudade da makamai da bayanan sirri wajen ci gaba da ayyukan ta'addancin da ke faruwa a kasar.