Iraqi: Gwamnati ta dakatar da Tashar Al Jazeera
Gwamnatin Kasar Iraki ta dakatar da tashar Telbijin din Al Jazeera ta kasar Qatar
Gwamnatin Iraqi ta umarci kafar yada labarai ta Al Jazeera da ta rufe ofishinta na birnin Bagadaza, tare da hana ma'aikatanta bayar da rahotanni a kasar.
Hukumomin sun zargi kafar yada labaran da karya dokar kafefen yada labarai ta kasar Iraqi, da suka hada da haramta yada duk wasu ayyukan kungiyoyin masu tada kayar baya.
A shekarar 2013 ma, Gwamnatin ta Bagdaza ta zarki Tashar Telbijin din Al Jazeera tare da wasu kafafen yada labarai na tauraron Dan Adam 9 da watsa labaran karya domin ingiza Al'umma ga rikicin kabilanci da kuma kokarin sanya tashin hankali tsakanin Al'ummar kasar
Al Jazeerar ta ce ta kadu matuka game da wannan mataki, kana ta musanta karya duk wata doka da ta shafi aikin kafafen yada labaran.