Syria Na Adawa Da Matakin Amurka, Na Tura Sojoji zuwa kasar
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4525-syria_na_adawa_da_matakin_amurka_na_tura_sojoji_zuwa_kasar
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria, ta bayyana rashin amincewar ta da matakin kasar Amurka, na tura sojoji zuwa kasar, wanda a cewar ta wannan matakin ya sabawa doka.
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
Apr 29, 2016 01:05 UTC
  • Syria Na Adawa Da Matakin Amurka, Na Tura Sojoji zuwa kasar

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria, ta bayyana rashin amincewar ta da matakin kasar Amurka, na tura sojoji zuwa kasar, wanda a cewar ta wannan matakin ya sabawa doka.

Wata sanarwa da ma'akatar harkokin wajen kasar ta fitar jiya Alhamis ta bayyana cewa, sojojin kasar Amurka 150 sun riga sun kutsa kai cikin yankin Rumailan na kasar ta Syria, wanda tuni Syria ta nuna damuwa game da hakan.

Mahukuntan Syria ne cewa, hakan barazana ce, duba da yadda sojojin suka shiga yankin ba tare da samun izini ba.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya sanar da tura sojoji 250 zuwa kasar Syria a ranar 25 ga watan nan, A cewarsa, an dau wannan mataki ne domin taimakawa dakaru masu adawa da gwamnati dake da sassaucin ra'ayi a kasar ta Syria wajen yaki da kungiyar IS.