Sojojin Gwamnatin Siriya Sun Rusa Sansanonin 'Yan Ta'addan Da'ish
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4543-sojojin_gwamnatin_siriya_sun_rusa_sansanonin_'yan_ta'addan_da'ish
Rundunar sojin Siriya da hadin gwiwar dakarun sa -kai sun kai waje jerin hare-hare kan sansanonin 'yan ta'addan kungiyar Da'ish da ke gabashin kasar tare da halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa.
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
Apr 29, 2016 13:15 UTC
  • Sojojin Gwamnatin Siriya Sun Rusa Sansanonin 'Yan Ta'addan Da'ish

Rundunar sojin Siriya da hadin gwiwar dakarun sa -kai sun kai waje jerin hare-hare kan sansanonin 'yan ta'addan kungiyar Da'ish da ke gabashin kasar tare da halaka 'yan ta'adda masu tarin yawa.

Shafin watsa labaran Al-Ahad na kasar Lebanon ya watsa labarin cewa: Sojojin gwamnatin Siriya da tallafin dakarun sa-kai sun yi dirar mikiya kan sansanonin 'yan ta'addan kungiyar Da'ish da suke yankunan garin Diru-Zur a gabashin kasar a yau Juma'a, inda suka halaka tarin 'yan ta'adda.

Har ila yau sojojin kasar ta Siriya da dakarun sa-kai da ke tallafa musu sun kwace iko da yankin Rakabiyya da ke gundumar Dirul-Asa'fir a garin Ghudah da ke gabashin lardin Rifi-Damasq bayan sun halaka 'yan ta'adda tare da fatattakan sauran da suka tsira da rayuwarsu.

A gefe guda kuma majiyar ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta sanar da cewa: 'Yan ta'adda sun kai harin da makami mai linzami kan karamin ofishin jakadancin kasar ta Rasha da ke garin Halab na kasar Siriya, amma harin bai janyo hasarar rai ba.