Harin ta'addanci a arewa da kudancin birnin Bagdaza
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4630-harin_ta'addanci_a_arewa_da_kudancin_birnin_bagdaza
Tashin wasu bama-bamai a Arewa da kudancin Birnin Bagdaza na kasar Iraki ya yi sanadiyar Mutawa da kuma jikkata 'yan kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:12+00:00 )
May 02, 2016 02:26 UTC
  • Harin ta'addanci a arewa da kudancin birnin Bagdaza

Tashin wasu bama-bamai a Arewa da kudancin Birnin Bagdaza na kasar Iraki ya yi sanadiyar Mutawa da kuma jikkata 'yan kasar.

Bom na farko ya tashi ne A anguwar Mashahid marecen jiya Lahadi a Arewacin Birnin Bagdaza, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar farar hula guda. sai kuma Bom na biyu da ya tashi a yankin Arab Jabur dake kudancin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar jikkata Mutane 3.

A Safiyar Jiya Lahadin wasu tagwayen motoci shake da bama-bamai sun tarwatse a garin Samawah babban birnin Jihar Almusanna, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane 23 tare da jikkata wasu 40 na daban.

Kashin da Kungiyoyin 'yan ta'adda ke sha a filin daga daga hanun Dakarun tsaron Iraki gami da na sa kai ya sanya su huce fishinsu kan fararen hula, inda a ko wata rana suke kai hare-haren ta'addanci a yankuna daban-daban na kasar

Tun daga watan Janairun shekarar 2014 ne kasar ta Iraki ta buskanci mayayar wasu yankuna daga Kungiyar 'yan ta'addar ISIS, lamarin da ya yi sanadiyar shahadar 'yan kasar da dama tare da raba dubban mutane da mahalinsu.