Mutane Da Dama Suka Rasa Rayukansu A Yakin Halab Na Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4753-mutane_da_dama_suka_rasa_rayukansu_a_yakin_halab_na_siriya
Majiyar labarai daga birnin Halab na kasar Siria sun bayyana cewa yan tabka yaki mai tsanani tsakanin sojojin
(last modified 2018-08-22T06:58:13+00:00 )
May 04, 2016 07:48 UTC
  • Mutane Da Dama Suka Rasa Rayukansu A Yakin Halab Na Siriya

Majiyar labarai daga birnin Halab na kasar Siria sun bayyana cewa yan tabka yaki mai tsanani tsakanin sojojin

Majiyar labarai daga birnin Halab na kasar Siria sun bayyana cewa yan tabka yaki mai tsanani tsakanin sojojin gwamnatin Bashar Al-asad da kuma na yan tawaye wanda ya kai ga mutuwar yan tawaye da dama. Majiyar sojojin kasar sun bayyana cewa yan ta'adda sun yi kokarin kwace wani ayanki a cikin birnin Amma sojojin gwamnati suka maida martayi wanda ya kai ga mutuwar yan ta'adda da dama da kuma fararen hula. Labarin ya kara da cewa an dau kusan shekara guda ba'a tabka yaki irin wannan tsakanin bangarorin biyu ba.

Wata majiyar yanntawaye ta bayyana cewa sun kashe sojojin gwamnatin siria 40, amma sun kasa rike wani yanki mai suna "Family" a birnin na Halab, bayan sun kwace shi daga hannun sojoji.

Majiyar ta kara da cewa sojojin sirian sun sami dauki daga mayakan hizbullah kafin su dawo da ikon gwamnatin a cikin garin.