Syria : An Tsawaita Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Da Kwanaki Uku A Halab
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i4867-syria_an_tsawaita_yarjejeniyar_tsagaita_wuta_da_kwanaki_uku_a_halab
Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da kwanaki uku a birnin Halep dake arewacin kasar Syria.
(last modified 2018-08-22T06:58:14+00:00 )
May 07, 2016 01:23 UTC
  • tsawaita tsagaita buda wuta a Syria
    tsawaita tsagaita buda wuta a Syria

Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da kwanaki uku a birnin Halep dake arewacin kasar Syria.

An dai tsawaita wannan yerjejeniyar ce bayan ta kwanaki biyu da aka cimma domin dakatar da buda wuta tsakanin dakarun gwamnatin Bashar al Assad da ‘yan tawayen kasar a Halab.

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce za'a ci gaba da tsagaita wutar a Halab da kuma Lattaquie.

Ita ma a nata bangare Amurka ta sanar da wannan fahimtar juna, kuma a cewar ta zata yi duk iyakacin kokarin ta na ganin hakan ta daure domin kawo karshen zubar da jini a duk wuraren dake da bukatar hakan.

kafin hakan dai bayanai sun nuna cewa bangarorin biyu sun mutunta yarjejeniyar tsagaita musayar wuta ta tsawon sa’oi 48 da suka cimma tun da farko bayan sun fuskanci matsin lamba daga kasashen na Rasha da Amurka.

Bayanai sun nuna cewa an dai shafe tsawon makwanni biyu ana gwabza fada tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawayen na Syria, lamarin da ya salwantar da rayukan mutane kusan 300.