Ganawar Mai Baiwa Jagora Shawara da Bashar Al-Asad
Mashawarcin Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran kan al'amuran kasa da kasa ya bayyana cewa Iran za ta yi amfani da dukkanin karfinta wajen yaki da ta'addanci a yanki.
A yayin ganarwar sa da Shugaban kasar Siriya yau Assabar a birnin Damuscus, Ali Akbar wulayati Mashawarcin Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran kan al'amuran kasa da kasa ya kara da cewa,in ban da juruya na Al'ummar Siriya da yanzu 'yan ta'adda sun cimma birnin Damuscus kuma Jumhoriyar musulinci ta Iran za ta ci gaba da taimakawa Al'ummar Siriya wajen yaki da 'yan ta'adda.
Wulayati ya ce yaki da ta'addanci domin sulhu da kuma tsaron yankin da ma duniya baki daya na da muhimancin gaske, babban manufar gwagwarmaya na yakar 'yan ta'addanci shi ne tabbatar da tsaro da sulhu A duniya.
A nasa bangare Shugaban kasar Siriya Bashar Al-Asad ya jinjiniwa Jumhoriyar musulinci ta Iran kan irin taimakon da take baiwa Al'umma Siriya, inda ya ce ya zuwa yanzu Magabatan Iran sun tsaya tsayin daga a bayan Al'ummar Siriya dangane da yakin da take yi da ta'addanci kuma ta taimakawa Siriya da dukkanin karfin da take da shi wajen yaki da ta'addanci.