Hallaka Sama da 'yan ta'addar Da'esh dubu uku a kasar Iraki
Ma'aikatar cikin gidan Iraki ta sanar da hallaka 'yan ta'addar ISIS sama da dubu uku a kasar
Kafafen watsa labaran kasar Iraki sun nakalto Ma'aikatar cikin gidan kasar a wannan Lahadi na cewa daga farkon wannan shekara zuwa yanzu Jami'an tsaron kasar sun hallaka 'yan ta'addar Da'esh ko kuma ISIS dubu uku da 452 a kasar.
Baya ga wannan adadi Ma'aikatar ta sanar da cewa Jami'an tsaron sun tsarkaka gariruwa, kauyuka gami da yankuna 318 da kungiyar ISiS din ta mamaye a baya.
Sa'ad Mu'in kakakin Ma'aikatar cikin gidan na Iraki ya kara da cewa Jami'an tsaron kasar sun samu nasarar warware bama-bamai a wasu manyan gine-gine da gidajen farar hula 283 da kungiyar ISiS din ta dasa sannan kuma sun tarwatsa maboya 181 na kungiyar ISIS din da wannan shekara.
Idan ba a manta ba dai tun a watan yulin shekarar 2014 ne kungiyar ISIS ta mamaye wasu jihohin kasar Irakin.
Dakarun tsaron kasar tare da taimakon Dakarun sa kai na kasar sun samu nasarar tsarkake yankuna da dama na jihar Anbar dake yammacin kasar tare da kuma wani bangare na yankin Nainuwa dake arewacin kasar daga mamayar 'yan ta'addar na ISIS.