Hallaka 'yan ta'adda a Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5278-hallaka_'yan_ta'adda_a_siriya
Dakarun tsaron Siriya sun hallaka 'yan ta'adda 50 a gefen garin Humus
(last modified 2018-08-22T06:58:17+00:00 )
May 17, 2016 01:12 UTC
  • Hallaka 'yan ta'adda a Siriya

Dakarun tsaron Siriya sun hallaka 'yan ta'adda 50 a gefen garin Humus

Kamfanin dillancin Labaram Tasnim na kasar Iran ya habarta cewa A jiya Litinin Dakarun tsaron kasar Siriya sun gano wani gungu na 'yan ta'adda da adadinsu ya kai 75 a gefen garin humus, inda suka kai masu farmaki tare da hallaka 50 daga cikinsu.

Rahoton ya ce Dakarun Siriya tare da hadin gwiwar Dakarun sa kai sun samu nasarar dakile wani hari da mayakan kungiyar ISIS suka kai kan jami'an tsaro a tsaunin Almazar dake gefen garin Humus, lamarin da ya janyo asara mai yawa ga bangaren 'yan ta'addar.

A ci gaba da kokarin tsarkake yankunan kasar, Dakarun Siriya sun samu nasarar tsarkake wasu hanyoyi dake gabashin gefen garin Humus.

Rahoton ya kara da cewa Dakarun tsaron Siriya sun samu nasarar shiga arewacin garin Alzara dake gefen garin hamah da mayakan kungiyar Jabhatu Nusra suka mamaye ranar Juma'ar da ta gabata.

Rahoton ya kara da cewa a wani farmako da Sojojin siriyan suka kai yammacin Jihar Dairu Zur sun samu nasarar kwato dandalin Fanurama daga hanun 'yan ta'adda bayan da suka hallaka akalla 'yan ta'adda ISIS 200 tare da jikkata wasu dama na daban.