An Kashe 'Yan Zanga-zanga Biyu A Iraki
Bayanai daga Iraki na cewa mutane biyu ne suka rasa rayukan su a lokacin da jami'an tsaro kasar ke kokarin tarwatsa masu zanga-zanga dake son shiga a muhimin wirin nan mai cikaken tsaro dake tsakiyar birnin Bagadaza.
ko bayan ga hakan akwai bayanai dake cewa mutane 57 ne suka jikkata a zanga-zanga ta jiya juma'a inda jami'an tsaro sukayi amfani da hayaki mai sa kwalla da ruwan masu karfi wajen tarwatsa masu zanga-zanga.
Jami'an tsaron sun ce sunyi harbin bindiga a sama don tsoratarda masu zanga-zanga, saidai wasu bayani sun nuna anyi harbi akan masu zanga-zanga lamarin da yayi sanadin mutuwar mutun biyu.
bayan dai sunyi nasara kusawa har cikin muhimmin wurin dake kunshe da gine-gine gwamnati da gidajen jami'an diflomatsiya, wasu daga cikin masu zanga-zanga sunn samu kusawa a offishin firiya ministan kasar Haidar Al-Abadi, inda suka kwashe dan lokaci.
Yau kusan makwani da dama da masu zanga-zanga ke fitowa kan tituna domin bukatar ga gwamnatin Al-Abadi ta dauki kwararen matakai na yaki da cin hanci da rashawa.
A cikin daren jiya firiya ministan kasar Al-abadi ya ce yana goyan bayan bukatun masu zanga-zanga a cikin lumana, aman yana adawa da duk wani mataki na mamaye ma'aikatun gwamnati.