Kungiyar Taliban Ta Nada Sabon Shugaba
Kungiyar taliban a kasar Afganistan ta nada Mawlawi Haibatullah Akhundzada a matsayin sabon shugaban ta.
kanfanin dilancin labaren faransa na AFP ya rawaito wata sanarwa daga kungiyar dake cewa ta nada Haibatullah Akhundzada a matsayin sabon shugaban ta bayan mutuwar Mullah Akhtar Mansour.
A kwanan nan ne dai jami'an leken asiri kasar Afghanistan suka tabbatar cewa an kashe jagoran Taliban din Mullah Akhtar Mansour, a harin da wani jirgin saman Amurka mara matuki ya kai a Pakistan, kusa da kan iyakar Afghanistan.
A sanarwar data fitar kungiyar ta ce sabon jagoran ta Akhundzada zai ci gaba da kare manufofin kungiyar.
Haibatullah Akhundzada zai maye gurbin Mullah Mansour wanda shi ne jagoran Taliban tun daga watan Juli na shekarar 2015.
kungiyar Taliban dai na cigaba da yin barazana ga jami'an Amurka da ke Afghanistan da kuma jami'an tsaron kasar da fararen hula.