Sojojin Iraki Sun Kwace kauyuka da dama a kusa da Fallujah.
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5755-sojojin_iraki_sun_kwace_kauyuka_da_dama_a_kusa_da_fallujah.
Kauyuka 11 ne Sojojin Iraki Su ka Kwace Daga Hannun 'yan ta'adda a kusa da Fallujah.
(last modified 2018-08-22T06:58:20+00:00 )
May 25, 2016 08:09 UTC
  • Sojojin Iraki Sun Kwace kauyuka da dama a kusa da Fallujah.

Kauyuka 11 ne Sojojin Iraki Su ka Kwace Daga Hannun 'yan ta'adda a kusa da Fallujah.

Tashar Telbijin din al-Iraqiyyah ta bada labarin da ke cewa; Sojojin sun yi nasarar korar 'yan ta'addar kungiyar Da'esh daga yankunan Nayif al-aly, da subaihat da al-lahib da alshawah. Sai kuma yankunan al-laifiyyah da al-shahaby da al-jumailah da su ke a gabacin birnin na Fallujah.

Kwanaki biyu da su ka gabata ne dai sojojin irakin da kuma dakarun sa kai, su ka shelanta farmakin kwato da garin fallujah daga hannun 'yan ta'addar Da'esh.