Gano Manyan Kabaruka A Tadammur Na Kasar Syria
May 26, 2016 07:35 UTC
Sojojin Syria Sun Gano Manyan Kabaruka A Kusa da Filin Saukar Jiragen Sama Na Tadammur.
Kamfanin Dillancin Labarun Sana na Syria daga yankin Homs ya nakalto cewa; Sojojin sun ci karo da kabarukan ne da su ke dauke da gawawwaki 31 a yayin da su ke share filin saukar jiragen saman garin na Tadammur da aka kori 'yan ta'adda.
Rahoton ya kuma tabbatar da cewa 'yan ta'addar kungiyar Da'esh, sun fille kawukan dukkanin mutanen da su ka turbude a cikin ramin.
Tags