Hallakar 'yan ta'adda a yankuna daban-daban na kasar Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i5836-hallakar_'yan_ta'adda_a_yankuna_daban_daban_na_kasar_siriya
A ci gaba da farmakin da Sojoji gami da dakarun sa kai ke kaiwa 'yan ta'addar ISIS da na jabhatunusra ,sun hallaka da dama daga cikin su a yankuna daban-daban na kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:20+00:00 )
May 27, 2016 05:44 UTC
  • Hallakar 'yan ta'adda a yankuna daban-daban na kasar Siriya

A ci gaba da farmakin da Sojoji gami da dakarun sa kai ke kaiwa 'yan ta'addar ISIS da na jabhatunusra ,sun hallaka da dama daga cikin su a yankuna daban-daban na kasar

Kamfanin dillancin Labaran Sana na kasar Siriya ya habarta cewa Dakarun Sama na Kasar sun kai farmaki kan mahadar 'yan ta'adda a garin Humus da Suwaida dake yamma da kudancin kasar, da kuma Dairu Zur na gabashin kasar tare da hallaka da dama daga cikin su, har ila yau harin yayi sanadiyar jikkata wani adadi mai yawa daga cikin 'yan ta'addar tare da lalata makamansu.

Jiragen Yakin na Siriya sun yi lugudar wuta a guraren 'yan ta'addar ISIS da Jabhatunusra a yankin Tadmur dake Jihar Humus.

A yankin Huma kuwa dake yammacin kasar, sama da 'yan ta'addar Jabhatunusra 50 ne suka hallaka sakamakon bata kashi da aka yi tsakanin su da Dakarun tsaro a yayin da suka kai hari a sansanin Sojin kasar dake kusa da Garin Ma'an.

Har ila yau Dakarun tsaron Siriya sun samu nasarar ceto wasu Mutane 20 da 'yan ta'addar suka sace a garin Alzara a wani farmaki da suka kaiwa 'yan ta'addar a gefen gudancin garin Hama,13 daga cikinsu Mata ne yayin da 5 kananen Yara ne.