Takadama Kan Nadin Sabon Shugaban Taliban
Wata takadama ta kunno kai a cikin kungiyar taliban, akan nadin sabon shugaban kungiyar, Haibatullah Akhundzada.
dayewa daga cikin mambobin kungiyar sun ce basa maraba da nadin na Akhundzada, kamar yadda kakakin kungiyar ya shaidawa manema labarai.
kakakin kungiyar ya ce Akhundzada dan asalin Kandahar wanda kuma mamba a offishin Mansour, bai taba taka wata rawa ta azo a gani ba a kungiyar ta Taliban kuma mutimin yaki bane be, hasali ma ba'a san shi ba a Afganistan.
wannan takadama dai ta kunno kai ne bayan da kungiyar ta tabbatar da mutuwar jagoranta Mollah Mansour, tare da nada Haibatullah Akhundzada a matsayin magajinsa a mukamin.
sauren mabobin dai suna zargin Akhundzada da cewa yana da alaka da hukumar lekan asirin kasar pakistan, tare da zargin sa da cewa ma yana da hannu a kisan Mollah Omar.
sabanin daya kunno kai a kungiyar yasa ta dare gida biyu, tsakanin masu goyan bayan Mansour da kuma Rassoul wadanda ke gwabza kazamin fada a wasu lokutan a wasu sassan kasa.
A ranar larabar data gabata ce kungiyar ta nada Haibatullah Akhundzada a matsayin sabon jagoran ta, bayan tabbatar da kisan Mollah Mansour a wani harin jirgin sama da Amurka ta kai a ranar 20 ga watan Mayu akan iyaka da Pakistan