Shahadar Dan Jarida a Garin Falluja na kasar Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6037-shahadar_dan_jarida_a_garin_falluja_na_kasar_iraki
'Yan ta'addar ISIS sun bindiga wani Dan Jarida a garin Falluja da hakan yayi sanadiyar shahadarsa.
(last modified 2018-08-22T06:58:22+00:00 )
May 31, 2016 06:17 UTC
  • Shahadar Dan Jarida a Garin Falluja na kasar Iraki

'Yan ta'addar ISIS sun bindiga wani Dan Jarida a garin Falluja da hakan yayi sanadiyar shahadarsa.

Ofishin 'yan jarida na kungiyar gwagwarmayar musulinci nujaba'a ya sanar da shahadar Abdul...Uryan Auda Dan Jaridar Wahidil-i'ilamul harbi na kungiyar a garin Falluja sanadiyar harbinsa da mayakan kungiyar ISIS suka yi.

A ranar 27 ga wannan wata na Mayu ne mayakan na ISIS sun halbi Abdul...Uryan Auda, sakamakon tsananin raunin da ya samu a daren jiya Litinin ya yi shahada.

A yau Talata ne aka yi jana'izar Abdul...Uryan Auda bisa halartar wasu daga cikin Dakarun sa kai na Hashdu-Sha'abi a jihar ta falluja.

Tun a farkon makun jiya ne aka fara kai farmaki na 'yanto garin Falluja daga hanun 'yan ta'addar ISIS bisa umarnin Piraministan kasar Irakin Haidar Ababi da kuma babban Hafsan Sojin kasar wanda a halin da ake ciki an shiga bangare na uku.