Afganistan : 'Yan Taliban Sun Kashe Fasinjoji 16
(last modified Tue, 31 May 2016 15:05:56 GMT )
May 31, 2016 15:05 UTC
  • Afganistan : 'Yan Taliban Sun Kashe Fasinjoji 16

kungiyar taliban ta dauki alhakin yin garkuwa da wasu fasinjojin masu yawa tare da kashe 16 daga cikin su a wannan Talata a yankin Kunduz na Afganistan.

A sanarwar data fitar kungiyar ta ce, ta kashe mutanen ne saboda su na yiwa gwamnatin Afganistan aiki, sanan kuma wannan manuniya ce ta cewa har yanzu fa ta na ci gaba da yakin da take mako guda bayan nadin sabon shugaban ta.

Wani jami'in 'yan sanda a yankin mai suna Shir Aziz Kamawal, ya shaidawa kanfanin dilancin labaran AFP cewa tsagerun sun tare motocin uku zuwa hudu suka kuma fitar da fasinjojin dake ciki, suka banbance su ta hanyar katinan su, kafin daga bisani su kashe 17, suka saki wasu daga cikin su, kana kuma sukayi garkuwa da wasu mutanen.

Shi ma da yake tabbatar da hakan kakakin gwamnatin ta Kunduz, Sayed Mahmoud Danish, ya ce 'yan taliban din sun kashe mutane 16, kana har yanzu suna garkuwa da wasu 30 na daban.

Wannan dai shi ne ta'adi mafi muni da kungiyar ta aiwatar tun bayan da Mollah Haibatullah Akhuzada ya maye gurbin mollah Mansur da wani jirgin Amurka maras matuki ya hallaka a Pakistan.