An Halaka Daruruwan "yan Ta'addan Takfiriyawa Na ISIS A Falluja
Kakakin rundunar sojin sa-kai na kasar Iraki Ahmad Asadi ya bayyana cewa, sun samu nasarar halaka daruruwan mayakan 'yan ta'addan Takfiriyya na ISIS a ba-ta kashin da ake yi da su domin kwace birnin Falluja daga karkashin ikonsu.
A zanatawarsa da kamfanin dillancin labaran Saumaria, Ahamd asadi ya bayyana, a cikin kwanaki kasa da 10 da suka gabata, a gumurzun da ake da 'yan ta'addan ISIS a gefen birnin Falluja, ya zuwa yanzu an halaka yan ta'addan na ISIS kimanin 665 tare da jikkata wasu daruruwan da kuma damke wasu.
Ahmad Asadi ya kara da cewa, dubban sojin sa kai ne suke taimaka ma sojojin Iraki a wannan yaki da suke yi da 'yan ta'adda da suka shigo kasarsu da sunan kafa abin da suke kira daular muslunci.
Ya kara da cewa yanzu haka dai akwai 'yan ta'addan ISIS kimanin 2000 a cikin garin na Falluja, wadanda suke yi garkuwa da fararen hula, kuma a cewarsa da yardar za su kammala tsarkake wannan birnin daga yan ta'addan na ba da jimawa, bayan katse dukkanin hanyoyin da suke samun taimako daga Qatar da Saudiyya zuwa garin na Falluja.