Tashin Bom A Arewacin Birnin Bagdaza
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6448-tashin_bom_a_arewacin_birnin_bagdaza
Mutum guda ya rasa ransa sannan wasu bakwai sun jikkata sanadiyar tashin Bom a Kudancin Bangaza fadar milkin Kasar Iraki
(last modified 2018-08-22T06:58:24+00:00 )
Jun 08, 2016 13:13 UTC
  • Tashin Bom A Arewacin Birnin Bagdaza

Mutum guda ya rasa ransa sannan wasu bakwai sun jikkata sanadiyar tashin Bom a Kudancin Bangaza fadar milkin Kasar Iraki

Rahotanni dake fitowa daga Kasar Iraki sun tabbatar da cewa A yau Laraba wani Bom ya tashi a Unguwar Husainiya dake arewacin Birnin Bagdaza, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum guda tare da jikkata wasu 7 na daban.

A bangare guda Jami'an tsaron Kurdawa na kasar Irakin sun sanar da dakile wani harin ta'addanci da 'yan ta'addar ISiS suka kai kamfanin Iskar Gaz na kasar Rasha dake yankin Kermayan na yankin Kurdawa a kasar ta Iraki.

Domin huce haushi a kan kashin da suke sha a hanun jami'an tsaron Iraki a Falluja, 'yan ta'addar ISIS din sun ruguza babban gurin tarihin nan na Bautar Nabo mai shekaru 2500.

Gurin bautar Nabo na a matsayin wani bangare da gabashin garin Tarihin nan na Namrud dake kudu maso gabashin garin Musil babban birnin Jihar Nainuwa mai nisan kilomita 400 daga Arewacin Birnin Bagdaza.

A watan Maris din shekarar 2015 da ta gabata, 'yan ta'addar ISIS din suka rusa garin Tarihin na Namrud.

Guraren tarihin kasar Iraki sun kasance shekara da shekaru ba tare da fuskantar wata illa ba, amma sai a 'yan shekarun nan bayan billar kungiyoyin 'yan ta'adda kamar su Da'esh ko ISiS aka fara rusa su.