(ISIS) Ta Dauki Alhakin Kai Hari A Iraki
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6481-(isis)_ta_dauki_alhakin_kai_hari_a_iraki
Rahotanni daga Iraki na cewa mutane akalla 18 ne suka rasa rayukan su, kana wasu 45 na daban suka raunana sakamakon wasu jerin hare-haren ta'adanci da kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaiwa a Bagadaza.
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 09, 2016 06:47 UTC
  • (ISIS) Ta Dauki Alhakin Kai Hari A Iraki

Rahotanni daga Iraki na cewa mutane akalla 18 ne suka rasa rayukan su, kana wasu 45 na daban suka raunana sakamakon wasu jerin hare-haren ta'adanci da kungiyar ISIS ta dauki alhakin kaiwa a Bagadaza.

Harin na farko an dai kai shi ne da wata mota a birnin Taji dake arewacin Bagadaza inda mutane a kalla bakwai suka riga gidan gaskia, kana wasu 18 suka raunana a cewar wata majiyar 'yan sanda.

Bayanai sun nuna cewa akwai jami'an tsaro da dama da harin ya rusa.

Harin na biyu kuwa an kai shi ne a daidai lokacin a wata kasuwa dake unguwar Jadida inda mutane 11 suka rasu, wasu kuma 27 suka raunana.

hare-haren kuma a cewar rahotanni sun hadasa barna mai yawa data shafi gidaje da kuma motoci.