Kasar Faransa Ta Baza Sojojinta Na Musamman A Arewacin Kasar Syria
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i6490-kasar_faransa_ta_baza_sojojinta_na_musamman_a_arewacin_kasar_syria
Faransa ta baza sojojinta a arewacin kasar Siria
(last modified 2018-08-22T06:58:25+00:00 )
Jun 09, 2016 10:52 UTC
  • Kasar Faransa Ta Baza Sojojinta Na Musamman A Arewacin Kasar Syria

Faransa ta baza sojojinta a arewacin kasar Siria

Gwamnatin kasar Faransa ta baza sojojinta na musamman a wani wuri a lardin Halab na kasar Siria. Majiyar ma'aikatar tsaro na kasar Faransa ta bayyana cewa sojojin kasar na musamman suna tallafawa kurdawan kasar Siria don ganin sun kori mayakan Daesh daga garin Manbij a cikin lardin Halab kusa da kan iyaka da kasar Turkia.

Majiyar ta kara da cewa sojojin Siria suna aiki tare da kungiyar yan tawaye ta the Syrian Democratic Forces (SDF) wacce ta kunshi Qurdawa da kuma larabawa, amma sojojin Faransa ba za su shiga yaki kai tsaye da kungiyar Daesh ba. Amma a jumma'ar da ta gabata ne ministan Tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian ya bada sanarwan cewa sojojin kasar ta Faransa suna tallafawa Qurdawa da kayakin yaki da kuma dabarbarun yaki a yakin da suke fafatawa da Daesh a larban Halab.

Har'ila yau majiyar kasar Amurka ta bayyana cewa kungiyar ta SDF ta kai faramaki kan mayakan Daesh a garin Na Manbij, inda mayakan Larabawa 3000 da na Qurdawa 500 sannan sojojin Amurka 300 na kasa sun tallafa masu a farmakin. Amma majiyar yan tawayen na SDF ta bayyana a yau Alhamis cewa sojojin Siria sun yi wa garin Manbij zobe daga Arewa, Gabas da kuma kudu.