De Mustura:Babu batun tattaunawar Sulhu kan kasar Siriya
Manzon Musaman na MDD kan Kasar Siriya ya ce a halin yanzu Majalisar ba za ta gudanar da taron Sulhu kan Siriyan A birnin Ganeva ba
A Jiya Alkhamis Staffan de Mistura Manzon Musaman na Majalisar Dinkin Duniya ya ce matukar dai bangarorin dake jayayya a siriyan ba su amince da kudirin kafa Gwamnatin hadin kai ba, to Majalisar ba za ta kira wani sabon zama ba.
De Mistura ya bayyana cewa wajibi ne a dage hijabi da ya hana ruwa gudu wajen kafa Gwamnatin rikon kwarya da nufin kawo karshen yakin shekaru biyar na kasar ta Siriya.
Har ila yau Staffan de Mistura ya sanar da sakin wasu daga 'yan adawar na Siriya, inda ya ce mai yiyuwa Gwamnatin ta dauki wannan kuduri ne saboda watan Ramadana.
Sannan ya bayyana cewa Gwamnatin kasar Siriya ta bada izini ga kungiyoyin da ke aikin agaji da su kai kayan abinci a wurare 19 da aka killace a cikin wannan watan da muke ciki.kuma yana kyautata zaton motocin kai kayan za su isa wuraren da ake tsammani a cikin lokaci. Dubban 'yan kasar Siriya ne dai ke fama da tsananin yunwa, kuma basa samun agaji daga kungiyoyin bada tallafi, sakamkon yadda gwamnati da 'yan tawaye suka killace yankunan da suke iko da su, a matsayin neman mika wuya ga abon kan gaba.