An gano wano kabarin gama gari a arewacin Iraki
An gano wani kabarin gama gari a jihar Salahuddin dake arewacin kasar Iraki
Kafar watsa labaran Masala ta kasar Iraki ta habarta cewa A jiya Assabar Dakarun tsaron kasar sun gano wani babban kabari da aka bisne Mutane da dama a cikin sa a kauyen Albujili na garin Takrit dake cikin jihar Salahuddin,inda aka gano gawawwakin mutane 10 daga mutane da aka bisne.
Sudai wadannan mutane 'yan kabilar Al-izza ne da aka yiwa kisan killa a lokacin da kungiyar ta'addancin nan ta ISIS ta mamaye yankin.
Dakarun tsaron kasar tare da taimakon kabilun yankin sun ce za su ci gaba da bankadon irin ta'asar da kungiyar ISIS ta aikata a kasar .
A watan yunin shekarar 2014 ne Kungiyar ISIS ta mamaye wani bangane da yamma da kuma arewacin kasar Iraki.
A cikin shekarar guda, Dakarun tsaron kasar tare da na sa kai sun samu nasarar tsarkake gariruwan Baiji, Takrit gami da Ramadi dake jihohin Salahuddin da Anbar na yammacin kasar ta Iraki.