Siriya : An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i661-siriya_an_cimma_yarjejeniyar_tsagaita_wuta
Matakin dai bai shafi yakin da akeyi da kungiyar (IS) da kuma al Nusra ba.
(last modified 2018-08-22T06:57:48+00:00 )
Feb 12, 2016 06:10 UTC
  • wasu sojojin Siriya
    wasu sojojin Siriya

Matakin dai bai shafi yakin da akeyi da kungiyar (IS) da kuma al Nusra ba.

Kasashen duniya sun amince su aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Siriya cikin mako mai zuwa bayan wani taro da suka gudanar a birnin Munich na kasar Jamus.

bayanai sun nuna cewa matakin tsagaita wutar ba zai shafi yakin da akeyi da kungiyar (IS) da kuma al Nusra ba.

kazalika masu ruwa da tsaki a rikicin kasar ta Siriya sun bukaci kai kayan agajin gaggawa zuwa Aleppo.

Sanarwar da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya karanta tace wata kungiya ta musamman a karkashin kasashen Rasha da Amurka zata sa ido dan tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar.