Iraki: Sojoji Sun Kusa Kame Tsakiyar Birnin Fallujah
Jun 13, 2016 03:17 UTC
Kwamandan Rundunar Fada Da Ta'addanci ya ce sojojin Iraki sun kusa isa tsakiyar birnin Fallujah.
Kamfanin Dillancin Labarun Spotnik ya ambato Abdulwahhab al-Saidy yana cewa sojojin da kuma hadin guiwa na mayakan sa-kai sun kutsa garin na Fallaujah ta kusurwowi daban-daban, sun kwace unguwar Shuhadaa wacce ta ke a kudu maso gabacin Fallujar.
A ranar 23 ga watan Mayu ne dai sojojin kasar ta Iraki su ka fara kai farmaki akan 'yan ta''adda.
Kawo ya zuwa yanzu dai dubban fararen hula ne mazauna garin na Fallujah, su ka sami damar ficewa.
Tags