Harin Birnin Beirut Da Tuhume-tuhumce
Bayan harin ta'addancin da aka kai a birnin Beirut, an fara yin zarge-zargen akan wadanda su ka kai shi.
Jaridar al-akhbar ta Lebanon ta ce; harin da aka kai a daren jiya a Beirut na nufi wani Banki ne mai suna: Bank Lubnan Wal Mahjar."
Editan Jaridar ta al-akhbar Ibrahim Amin, ya ce; Wadanda su ka kai harin manufarsu ta fi karfin haddasa asarar.
Har ila yau, Ibrahim Amin, ya bayyana yadda a cikin kasar ta Lebanon ake yin sharhi akan harin, wanda shakka babu ba shi da wata ma'ana.
A cikin kasar ta Lebanon wasu masharhanta da bangarorin siyasa, sun fara dora alhakin akan kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah, bisa abinda su ka ce; yana da alaka saboda kakabawa Hizbullah takunkumi."
Editan Jaridar ta al-akhbar ya kuma kara da cewa; kungiyar ta Hizbullah tana da masaniya akan cewa; Ba ta da maslaha a cikin ayyuka irin wadannan.