Syria : MDD Na Fatan Shigar Tallafi A Al-Waer
Gwamnatin Syria ta amunce da shigar da kayan agaji a unguwar Al-ware dake karkashin ikon 'yan tawaye a birnin Homs dake tsakiyar kasar.
kakakin ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD, Jens Laerke ya shaidawa manema labarai cewa sunan fatan shigar da ayarin motocin farko dake dauke da tallafi tun a wannan Alhamis, bayan samun izini daga mahukuntan Damascos.
Yau dai watanni uku kenan marabin da a shigar da kayan agaji a wannan unguwa ta Al-Waer a cewar jagoran kula da ayyukan jin kai na MDD a Syria.
A jimulce, mutane kimanin 600.000 ne ke zaune yanzu haka a wuraren da ake rikeda a Syria.
Tun dai farkon rikicin Syria a cikin shekara 2011, mutane sama da 280.00 ne suka rasa rayukan su, kana wasu milyoyi suka bar gidajen su saboda yakin daya daidaita kasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a karshen watan Afrilu, a yayin da kuma tattaunawar neman sulhu da ake fatan cimmawa ta koma a ruwa.