Afganistan : Hare-hare Sun Kashe Mutane 25 A Kaboul
(last modified Mon, 20 Jun 2016 17:27:17 GMT )
Jun 20, 2016 17:27 UTC
  • Afganistan : Hare-hare Sun Kashe Mutane 25 A Kaboul

Rahotanni daga Afganistan na cewa mutane 25 ne suka rasa rayukan su a wasu jerin hare-haren kunar bakin wake a birnin Kaboul da kuma kudu maso gabashin kasar.

Daga cikin dai wadanda suka rasa rayukan su hada da wasu ma'aikatan tsaro 'yan asalin kasar guda Nepal 14,

Ko baya ga wadanda suka mutu akwai wasu 'yan Nepal biyar da suka jikatta sai kuma wasu 'yan Afganistan guda hudu.

Harin mafi muni dai ne na farko wanda wani dan kunar bakin wake ya kai kan wata motar bas dake kan hanyar zuwa Kabul zuwa jalalabad dake gabashin kasar..

Jin kadan bayan hakan ne kuma wani bom ya tashi a lokacin da wani ayarin motoci wakilin yankin ke wucewa inda mutum daya ya mutu wasu hudu kuma suka raunana.

Saidai har kawo yanzu ba'a kai ga sanin takamaimai wa keda alhakin kai wadanan hare-haren, kasancewar kungiyar Taliban da kuma kungiyar IS duk sun fitar da sanarwar daukan nauyin kai hare-haren.

Wannan dai shi karo farko da kai hare-haren a wannan kasa tun dai bayan matakin Amurka na kara karfafa ayukan ta a wannan kasa ta Afganistan.