Firaministan Iraki Ya Isa Birnin Fallouja Da Sojoji Suka Kwato
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i7288-firaministan_iraki_ya_isa_birnin_fallouja_da_sojoji_suka_kwato
Firaminstan Iraki, Haider al-Abadi ya isa birnin Fallouja da dakarun kasar suka kwato daga hannun 'yan ta'adan (IS).
(last modified 2018-08-22T06:58:30+00:00 )
Jun 26, 2016 11:15 UTC
  • Firaministan Iraki Ya Isa Birnin Fallouja Da Sojoji Suka Kwato

Firaminstan Iraki, Haider al-Abadi ya isa birnin Fallouja da dakarun kasar suka kwato daga hannun 'yan ta'adan (IS).

Mr al-Abadi yayi kira ga al'ummar kasar dasu gudanar bikin murna akan wannan nasara da dakarun kasar sukayi ta kwato birin na Falluja.

 

Gidan talabijin din kasar ya nuno hoto Mr Abadi rataye da tutar kasar wuya a harabar asibitin birin yana mai kira ga dukkan al'ummar kasar a duk inda suke dasu nuna murna akan wannan nasara.

 

A cewar wani Janar din sojin kasar sojoji sun fatattaki 'yan ta'adan daga wani waje da ke kusa da Golan.

 

kuma wannan shi ne yanki na karshe da ke karkashin ikon 'yan ta'adan na IS a cewar janar din, wanda yake nufin an kammala kwato Fallujah.

 

Wannan dai babbar nasara ce ga dakarun kasar ta Iraki da suka kaddamar da farmaki kan 'yan ta'adan na IS da sukayi kaka-gida a wannan yankin.