Labanon : Sojoji Sun Dakile Harin (IS)
Rundinar sojin kasar Labanon ta sanar da cafke mambobin kungiyar 'yan ta'ada Da'esh biyar wandanda a cewar ta ke shirin kai hare-hare a cikin kasar.
Sanarwar da rundinar sojin kasar ta fitar yau Alhamis ta ce mutanen na shirin kai hare-hare ne a wuraren dake da cinkoson jama'a a Beyrout.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan wasu jerin hare-hare a kusa da iyakar kasar da Syria.
Kasar Labanon dai na fuskantar barazana 'yan ta'adan IS da sukayi kaka-gida a wasu sassan kasar ta Syria.
ko a wannan Litinin data gabata wasu jerin hare-haren kunar bakin wake a kauyen Al-Qaa sunyi sanadin mutuwar mutane biyar tareda jikkata wasu 28.
kawo yanzu dai rundinar ta ce tana ci gaba da bincike akan mutanen ko walla-Allah za'a samu wasu karin bayanai daga garesu.