Iraki : Anyi wa (IS) Mumunar Barna A Fallujja
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i7477-iraki_anyi_wa_(is)_mumunar_barna_a_fallujja
Rundinar sojin Iraki ta ce fiye da 'yan ta'adan (IS) 150 ne suka hallak bayan ruwan wuta da akayi musu a lokacin da suke kokarin sulalewa daga birnin Falluja.
(last modified 2018-08-22T06:58:31+00:00 )
Jun 30, 2016 11:31 UTC
  • Iraki : Anyi wa (IS) Mumunar Barna A Fallujja

Rundinar sojin Iraki ta ce fiye da 'yan ta'adan (IS) 150 ne suka hallak bayan ruwan wuta da akayi musu a lokacin da suke kokarin sulalewa daga birnin Falluja.

Sanarwar da rundinar ta fitar ta kuma ce anyi kaca-kaca da mototin 'yan ta'adan iri daban daban manya da kananan su da yawan su ya kai 260 duk dai a lokacinda suke kokarin tserewa daga birnin na Fallouja daga ranar Talata zuwa yanzu.

Ma'aikatar tsaron Iraki ta nuna hoto bidiyon yadda lamarin ya auku inda akayi amfani da jiragen sama yaki masu saukar ungulu da kuma jiragen yaki.

Ita ma dai ma'aikatar tsaron Amurka ta fitar da wani labari makamancin wannan inda ta ce kawacen sojojin da take jagoranta a kasra ta Iraki yayi kaca-kaca da wani ayarin motoci da yawan su ya kai 175, aman ba tare da bada adadin mutanen da aka hallaka ba a wannan farmakin.

Bayanai dai sun ce jiragen yakin sun kai farmaki kan ayarin motocin 'yan ta'adan daya kunshi daririwan motoci da wasu suka dushi kudu maso yamma da wasu da sukayi arewa maso yamma.

A kwanan nan dai rundinar sojin kasar Iraki ta sanar da kwace birnin Falluja daya jima karkashin ikon 'yan ta'adan na IS.