Jawabin Sayyid Hasan Nasrull...dangane da Ranar Qudus
Babban saktaren Kungiyar Hizbull...ta kasar Labnon ya ce manufar Ranar Duniya ta Qudus Raya ambaton Qudus da kuma tunatarwa Al'ummar musulmi alkawarin da suka dauka a kan Qudus
A yau ne Al'ummar musulmi a sassa daban daban na Duniya suka gudanar da zanga-zanga raya ranar Qudus kamar yadda aka gudanar a nan kasar Iran
A kasashen Iraki, Bahren, Afganistan, Pakistan, Indiya , Labnon milyoyin Mutane suka gudanar da wannan zanga-zanga.
Yayin jawabin da ya gudanar a marecen Yau, Babban saktaren kungiyar Hizbull...ta kasar Labnon ya tabbatar da cewa Ranar Duniya ta Qudus, Rana ce ta raya tahiri tare da karya lagon Isra'ila wacce Imam Khumaini (k.s) wanda ya asassa jumhoriyar musulmi ta Iran ya sanya a ranar Juma'a ta karshen ko wani watan Ramadana.
Sayyid ya ce daga tekun Meditrenia har zuwa gadar tekun Jodan guri ne da aka mamaye kuma aka kwace daga Ahlinsa na asali , lokaci ba zai sanya a amince da HKI ba ,hanya guda cilo ta kare da kuma goyon bayan Al'ummar Palastinu ita ce hanyar gwagwarmaya.
Yaayin da ya koma kan wasu kasashen yankin da suka amince da halarcin Isra'ila ya ce bayan amincewa da wannan haramcecciyar kasa, sun hada kai da ita wajen yakar kungiyoyin gwagwarmaya.
Yayin da koma kan irin ta'addancin da HKI tare da hadin kan masarautar Ali sa'oud ke yi a kasashen musulmi, Sayyid Hasan Nasrull..ya ambato kisan killan da Dakarun tsaron Najeriya suka yiwa 'yan uwa almajirai Shekh Ibrahim Elzakzaky kusan dubu guda a garin Zaria tare da hadin kai kasashen Amurka, Isra'ila gami da masarautar Ali-sa'oud.
Sayyid ya ce rawar da kasar Amurka gami da HKI ke takawa a kasashe kamar su Siriya, Yemen, Bahren gami da Libiya ya hana a samu mafuta sai dai kara rura wutar yaki suke yi, halartar 'yan ta'adda a taron baya-bayan nan na Herzliya a HKI shike tabbatar cewa magaban tel-Aviv na da hanu dumu-dumu wajen yakin kasar Siriya.