An Fara Zaman Makoki A Iraki
An fara zaman makokin kwana uku a kasar Iraki, bayan kazamin harin da aka kai kan wani gidan abinci a Bagadaza babban birnin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 119.
Fira ministan kasar ne Haider Al-Abadi ya sanar da shiga zaman makokin daga yau Litinin, tare da shan alwashin mayar da martani mai tsanani ga wadanda suka kisa wannan harin.
Harin wanda shi ne irin sa mafi muni a cikin shekara nan ya yi kuma sanadin jikkatar mutane 180 a cewar ma'aikatar cikin gidan kasar ta Iraki.
Kungiyar 'yan ta'ada (IS) ce ta dauki alhakin kai harin kunar bakin waken a wani titin kasuwar Karada wajen sayar da abinci, inda a nan ne mutane suka fi mutuwa.
Harin na biyu kuma an kai shi ne a arewacin Bagadaza, inda mutane biyar suka mutu.
Wadanan hare-hare dai na zuwa ne mako guda bayan kwace birnin Falluja daga hannun 'yan ta'adan na (IS)