Sojojin Amurka Zasu Ci Gaba Da Kasancewa A Afganistan
(last modified Wed, 06 Jul 2016 17:32:44 GMT )
Jul 06, 2016 17:32 UTC
  • Sojojin Amurka Zasu Ci Gaba Da Kasancewa A Afganistan

Shugaban Amurka Barack Obama ya sanar a wannan laraba cewa sojojin kasarsa zasu ci gaba da kasancewa a Afganistan har zuwa karshen wa'adin mulkinsa.

A farkon shekara 2017 mai zuwa ce wa'adin mulkin Obama ke kawo karshe, kuma a cewar saboda yanayin da ake ciki a Afganistan sojojin Amurka 8.400 zasu ci gaba da aiki.

A cewar Obama har yanzu 'yan Taliban na ci gaba da zama babbar barazana, kuma ganin yadda sojojin Afganistan din basu kotsa ba yadda zasu murkushe 'yan taliban din sojojin Amurka zasu ci gaba da kasancewa a Afganistan.

Mr Obama ya kara da cewa wannan matakin daya dauko zai budewa magajinsa wasu hanyoyi na kawo karshen yaki a kasashen Afganistan da Iraki kamar yadda ya yi alkawari.