Sakataren Tsaron Amurka Na Ziyara A Iraki
Yau Litinin, sakataren tsaron Amurka, Ashton Carter ya isa birnin Bagadaza na Iraki inda zai tattaunawa da firayi minista Haider al-Abadi akan yaki da kasar keyi da 'yan ta'ada na (IS).
kazalika bangarorin biyu zasu tabo batun kwace ikon birnin Mossul daga hannun 'yan ta'dan na IS wanda ya kasance wani babban ci gaba a yunkurin murkushe 'yan ta'adan.
Mr Carter zai yi kuma amfani da wannan damar domin ganawa da kwamandodin sojin kasar sa dake dafawa a yakin da ake da 'yan ta'adan.
Wannan ziyara ta Mr Carter na zuwa ne kwana biyu kacal da sojojin Iraki suka kwace wani sansanin jiragen sama dake kudancin Mossul wanda zai taimaka matuka wajen kwato birnin dake zamen na biyu mafi mahimanci dake karkashin ikon 'yan ta'adan tun a cikin watan Yuni shekara 2014.