An Kashe Wani Babban Kwamandan (IS) A Iraki
Jul 14, 2016 07:27 UTC
An kashe wani babban kwamandan 'yan ta'adan (IS), mai suna Omar al-Shishani a kasar Iraqi kamar yadda wata kafar labaran 'yan ta'adan mai suna Amaq ta sanar.
Saidai kafar yada labarai ta Amaq ba ta yi Karin haske ba game da hakikanin ranar da aka hallaka kwamandan wanda aka fi sani da suna "Omar le Tchétchène"
Wanda dai ya kasance babban koma baya ga kungiyar a daidai lokacin da ake kokarin kwace birnin Mosul.
A watan Maris ne ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta ce, dakarun kasar sun yi nasarar kashe al-Shishani amma bata sanar da yadda aka kashe shi ba da kuma inda hakan ya faru.
Tags