Ana zaman makoki a Afganistan
An fara zaman Makoki na mutuwar mutane sama da 80 a Afganistan
Al'ummar kasar Afghanistan na zaman makoki a ranar Lahadi bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai birnin Kabul ranar Asabar da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 80.
Fiye da mutane 230 kuma suka samu raunuka a harin da aka kai cikin masu zanga-zanga 'yan kabilar Hazara marasa rinjaye, wadanda galibin su 'yan shi'a ne.
Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai harin.
Shugaba Ashraf Ghani ya ce ya yi matukar bakin ciki da harin, inda ya sha alwashin daukar fansar mutanen da aka hallaka.
Ofishin MDD a Afghanistan ya bayyana harin a matsayin laifin yaki.
A bangare guda, Zabihullahi Mujahid kakakin kungiyar taliban ya sanar da cewa manbobin kungiyar su ne suka kai hari a guraren jami'an tsaron Arabkiyan masu goyon bayan Gwamnatin Ashraf Gani a yankin Aklaq na kauyen Derzab dake cikin jihar Jorjan inda suka halaka tare da jikkata uku daga cikin su.