Gwamnatin Iraki Ta Jaddada Bukatar Ficewar Sojojin Turkiyya Daga Cikin Kasarta
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i8662-gwamnatin_iraki_ta_jaddada_bukatar_ficewar_sojojin_turkiyya_daga_cikin_kasarta
Ministan harkokin wajen kasar Iraki ya jaddada bukatar ganin gwamnatin Turkiyya ta hanzarta janye sojojinta da suke mamaye da wani yankin kasar Iraki tun a watan Disamban shekarar da ta gabata.
(last modified 2018-08-22T06:58:39+00:00 )
Jul 25, 2016 13:42 UTC
  • Gwamnatin Iraki Ta Jaddada Bukatar Ficewar Sojojin Turkiyya Daga Cikin Kasarta

Ministan harkokin wajen kasar Iraki ya jaddada bukatar ganin gwamnatin Turkiyya ta hanzarta janye sojojinta da suke mamaye da wani yankin kasar Iraki tun a watan Disamban shekarar da ta gabata.

A jawabinsa a zaman taron kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a birnin Nouakchott fadar mulkin kasar Mauritaniya a yau Litinin; Ministan harkokin wajen kasar Iraki Ibrahim Ja'afari ya bukaci kasashen Larabawa da su dauki matakin sanya matsin lamba kan gwamnatin Turkiyya domin ganin ta janye sojojinta da ta jibge a cikin kasar Iraki.

Ibrahim Ja'afari ya kara da cewa: Matakin da gwamnatin Iraki ta dauka na girmama hakkin makobtaka baya nufin zata yi shiru kan mamaye mata kasa. Tun a cikin watan Disamban shekarar da ta gabata ce ta 2015 gwamnatin Turkiyya ta dauki matakin jibge daruruwan sojojinta a sansanin sojin kasar Iraki na Ba'ashiqah da ke kusa da garin Mosel bisa da'awar yaki da kungiyar ta'addanci ta Da'ish kuma Turkiyya ta yi kunnen uwan shegu kan duk wani kiraye-kirayen da duniya ke ci gaba da yi mata na neman janye sojojin daga cikin kasar ta Iraki.