Syria : Harin (IS) A Qamichli Ya Kashe Mutane Akallah 44
Rahotanni daga Syria na cewa mutane a kalla 44 ne suka rasa rayukan su kana wasu 140 suka raunana a wani harin bom da aka kai da wata babbar mota a birnin Qamishli na galibi Kurdawa.
Tuni kungiyar 'yan ta'ada ta (IS) ta ce ita keda alhakin kai harin, a matsayin maida martani na hare-hare da kawacen Kurdawa dana larabawan syria dsuka kai masu a birnin Minbej dake arewacin kasar.
A wata sanarwa data fitar, kungiyar ta ce wani dan kunar bakin wake ne ya kai hariin a cikin wata babbar mota makare da boma-bomai.
Wasu rahotanni na daban sun ce akwai yiwuwar adadin mutanen da suka rasa rayukan su ya wuce haka.
Wanan dai shi ne hari mafi muni daya shafi wannan birni dake arewa maso gabashin kasar Syria inda dakarun Kurdawa dana gwamnatin Syria ke raba iko, tun dai bayan barkewar yaki a shekara 2011 a wannan kasa ta Syria.