"Yan ta'adda Sun Hana Farare Hula ficewa Daga Birnin Halab
Jul 29, 2016 06:50 UTC
Mutane Kadan Ne Su Ka Fice Daga Birnin Halab, Bayan Da 'yan ta'adda su ka hana mafi yawanci fita.
Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya ce; mutane kadan ne su ka sami damar ficewa daga garin Halab, bayan da 'yan ta'adda su ka hana mafi yawanci ficewa.
A jiya alhamis ne gwamnatin Syria ta sanar da bude hanyoyin da za su bai wa fararen hula ficewa daga cikin birnin, da kuma masu dauke da makamai da su ke da sha'awar mika makamansu.
A daren jiya, jiragen yakin gwmanatin syria sun yi ruwan wuta akan sansanonin 'yan ta'addar da ke gabacin birnin na Halab.
A yau juma'a 'yan ta'addar sun rufe hanyoyin da za su bada dama ga masu fita daga cikin birnin.
Tags