Ci Gaba Da Tsare Mutane Sakamakon Kokarin Juyin Mulkin Kasar Turkiyya
Ministan cikin gidan kasar Turkiyya Efkan ya sanar da cewa ya zuwa yanzu jami'an tsaron kasar sun kama mutane dubu 18 kamar yadda kuma aka sanya wa wasu mutane dubu 50 takunkumi hana barin kasar biyo bayan kokarin juyin mulkin da bai ci nasara ba da aka yi a kasar a daren ranar 15 ga watan Yulin nan.
Rahotanni daga kasar Turkiyyan sun bayyana cewar mutanen da aka kama da kuma ci gaba da tsare su din sun kumshi kusan dukkanin bangarori na al'ummar kasar ne da suka hada da sojoji, jami'an ma'aikatar shari'a, cibiyoyin ilimi da dai sauransu da ake zargin cewa suna da alaka da babban dan adawar kasar Fethullah Gulen da kuma kungiyarsa da aka fi sani da Hizmet.
Har ila yau rahotannin sun ce duk da cewa a halin yanzu an samu raguwar kama mutane da jami'an tsaron Turkiyyan suke yi idan aka kwatanta da yadda suke yi a ranakun farko-farko na yunkurin juyin mulkin da bai ci nasara din ba, to amma dai har ya zuwa yanzu ana ci gaba da kama mutane da kuma takurawa wasu rayuwarsu.
Irin wannan dirar mikiya da gwamnatin Rajab Tayyib Erdogan take yi wa 'yan adawa a kasar da kuma irin iko mara haddi da shugaba Erdogan ya ba wa kansa sakamakon kafa dokar ta baci da yayi a kasar hakan ne ya sanya masu sukar gwamnatin a wajen kasar kai ma a cikin kasar da kuma wasu cibiyoyi da kafafen watsa labarai suka fara sanya shakku kan hakikanin faruwar juyin mulki da bayyana shi a matsayin wani shiri kawai da aka shirya da nufin ganin bayan 'yan adawa musamman bisa la'akari da cewa ya zuwa yanzu gwamnatin ta dakatar da ayyukan sama da tashoshin talabijin, jaridu, kafafen watsa labarai da gidajen radiyoyi 100 a kasar.
Irin wannan adadi mai yawan gaske na mutanen da aka kama da kuma tuhumar da gwamnatin Erdogan din take yi wa babban dan'adawa kuma babban malamin kasar, Fethullah Gulen na shirya juyin mulkin, bugu da kari kan batun yadda za a rufe gawawwakin sojojin da suka shirya juyin mulkin da aka kashe su, dukkanin wadannan suna daga cikin batutuwan da a halin yanzu suka zamanto babban kalubale ga gwamnatin Turkiyyan da kuma haifar da kace-nace tsakaninta da gwamnatocin kasashen Yammaci.
Daga cikin irin wadannan kalubalen da ya kunno kai tsakanin gwamnatin Turkiyyan da kawayenta na kasashen Yammacin ana iya ishara da kama wasu sojoji da suka kasance tamkar masu kulla alaka tsakanin sojojin Turkiyyan da Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon saboda zargin da ake musu da hannu cikin juyin bayan da gwamnatin ta zargi daya daga cikin manyan jami'an sojin Amurka, wato Janar Joseph Votel wanda da hannu cikin shirya juyin mulkin, lamarin da lamarin da Janar din ya musanta da kuma yin kakkausar suka ga wannan siyasa ta gwamnatin Turkiyya.
Wani batun da kuma ya kara janyo kace-nace a ciki da wajen kasar Turkiyyan shi ne batun rufe gawawwakin sojojin da suka shirya juyin mulkin da aka kashe bayan sanarwar da gwamnatin Erdogan din ta yi na rufe su a wata makabarta da suka ba ta sunan "Makabartar Maciya Amana", lamarin da wasu hatta a cikin gidan Turkiyyan suke ganinsa a matsayin cin mutumci da kuma take hakkokin iyalan mamatan na bisne gawawwakin 'yan'uwansu yadda suke so.
Ya zuwa yanzu dai irin mu'amalar da gwamnatin Turkiyyan take yi da batun juyin mulkin ya sanya da dama suke ganin za ta iya fuskantar gagarumin kalubale a nan gaba kadan musamman idan aka yi la'akari da yadda wasu 'yan majalisar kasar suka fara kokawa kan abin da ke gudana da kuma sanya shakkunsu kan abin da suka kira boyayyiyar siyasar shugaba Erdogan kan sojojin kasar. 'Yan majalisar dai suna bayyana abin da Erdogan din yake yi a matsayin wani kokari na tabbatar da ikonsa a kan sojoji da kuma cibiyar leken asiri da tsaro na kasar don cimma manufofinsa na siyasa, lamarin da suke ganin zai iya sanya kasar cikin wani irin yanayi na rashin tabbas.