Iraki : Kwamandojin (IS) Sun Gudu Tare Da Iyalensu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i8947-iraki_kwamandojin_(is)_sun_gudu_tare_da_iyalensu
Hukumomi a kasar Iraki sun sanar da cewa kwamandojin kungiyar 'yan ta'ada ta (IS) sun gudu tare da iyalansu daga birnin Mosul.
(last modified 2018-08-22T06:58:41+00:00 )
Jul 31, 2016 09:58 UTC
  • Iraki : Kwamandojin (IS) Sun Gudu Tare Da Iyalensu

Hukumomi a kasar Iraki sun sanar da cewa kwamandojin kungiyar 'yan ta'ada ta (IS) sun gudu tare da iyalansu daga birnin Mosul.

Ministan tsaro kasar ta Iraki ne Khaled al-Obeidi ya bayyana hakan a wata hira da gidan talabijin din kasar ''Iraqiya"' tare da cewa dayewa daga kwamandodin IS din sun sayar da kaddarorinsu sun kuma gudu daga Mosul, inda suka nufi iyaka kasar da Syria.

Birnin Mosul, dai shi ne birni na biyu da sojojin kasar Iraki suka shafe watanni da dama suna kokarin kwatowa daga hannun 'yan ta'ada na (IS).

A wani labari kuma firaministan kasar Haider al-Abadi ya gana a wannan Lahadin da kwamadan hulda tsakanin sojojin Amurka, Joseph Dunford a Bagadaza inda suka tattauna kan tsare-tsaren kwato birnin Mosul dake zamen cibiyar 'yan ta'adan na (IS).

Saidai a cewar rundinar sojin kasar Iraki aikin kwato birnin Mosul ba za'a shige shi kai tsaye ba, kasancewar dubban fararen hula dake kange a cikinsa, lamarin da zai iya janyo bala'i ba kadan ba.