MDD, Ta Gayyaci Gwamantin Syria A Hukumance, A Tattaunar Sulhu
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i8950-mdd_ta_gayyaci_gwamantin_syria_a_hukumance_a_tattaunar_sulhu
Majalisar Dinkin Duniya ta mikawa gwamnatin Syria gayyata shiga sabon zagayen tattaunawar sulhu da za'a yi a karshen watan Agusta mai shirin kamawa tare da 'yan adawa na kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:41+00:00 )
Jul 31, 2016 10:28 UTC
  • MDD, Ta Gayyaci Gwamantin Syria A Hukumance, A Tattaunar Sulhu

Majalisar Dinkin Duniya ta mikawa gwamnatin Syria gayyata shiga sabon zagayen tattaunawar sulhu da za'a yi a karshen watan Agusta mai shirin kamawa tare da 'yan adawa na kasar.

Mukadashin mai shiga tsakani a rikicin kasar ne na MDD, Ramzy Ezzeldin Ramzy, ya mika wannan gayyata a hukumance ga gwamnatin ta Syria, wace tuni ta bayyana aniyarta ta shiga tattaunawar.

Ministan harkokin wajen Syria, Fayçal Moqdad wanda ya karbi gayyatar daga hannun wakilin na MDD, ya bayyana cewa suna maraba da wannan tayin kuma sunda niyyar shuga tattaunawar, mudun dai ta tsakanin 'yan kasar ta Syria ce ba tare da tsoma bakin wata kasa ba.

A ranar Talata data gabata ce wakilin MDD kan rikicin kasar ta Syria, Staffan de Mistura ya bayyana fatansa na shirya zagaye na uku na tattaunawa sulhu tsakanin gwamnatin da 'yan adawa na Syria a karshen watan gobe.

Kafin hakan dai an gudanar da tattaunawa sulhu har sau biyu a cikin wannan shekara ba tare cimma wata matsaya ba.

Wannan tayin tattaunawar dai na zuwa ne a daidai lokacin 'yan tawayen na Syria ke cikin tsaka mai wuya, musamen a yankin Aleppo inda dakarun gwamnatin Syria suka mamaye unguwanni da dama.