Iraki Ta Gargadi Saudiyya Akan Atisayen Soja
Feb 17, 2016 09:07 UTC
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iraki ya gargadi Saudiyya da kada ta kuskura ta keta hurumin kasarsa a yayin atisayen sojan da ta ke yi.
Tashar Telbijin din al-mayadden da ke watsa labarunta a kasar Lebanon ta ambato minstan harkokin Wajen kasar Iraki, Dr. Ibrahim Ja'afari da ya ke ziyarar aiki a kasar Tunisiya ya nuna kin amincewarsa da yin atisayen sojan na Saudiyya akan iyaka da Irakin.
Saudiyyar da wasu kasashe kusan 20 suna gudanar da atisayen soja akan iyaka da kasar Iraki.
Da ya ke magana akan halin da kasar Libya ta ke ciki, Ministan harkokin Wajen na Iraki ya ce; muna nuna cikakken goyon bayanmu akan duk wani taimako na kasa da kasa domin samun galaba akan ta'addanci.
Tags