Iraki : An Raunana (IS) A Mosul, Inji Amurka
Ma'aikatar tsaron Amurka, Pantagone ta ce an karya laggon kungiyar (IS), sannan kungiyar na nuna kasawa a Mosul birnin na biyu na kasar Iraki wanda ke zamen tungar 'yan ta'adan.
kamar yadda kakakin kawacen yaki da kungiyar a Iraki, kanal Chris Garver ya sanar ya ce kungiyar ta raunana sosai kuma suna da bayanai dake nuna yadda kwamandodin kungiyar suka fusata suna yanka magoya bayansu saboda kasa tabaka komai a fagen daga a birnin Mosul.
Jami'in ya kara da cewa dama an fuskanci hakan a cen baya a biranen Falluja da Ramadi gabanin kwato su daga hannun 'yan ta'adan.
Saidai duk da hakan jama'in ya ce kokarin kwato birnin Mosul a 'yan watanni masu ba zai zamanto abu mai sauki ba.
Yau watanni da dama kenan da kawacen dakarun Iraki dana Kurdawa, dake samun dauki hare-haren sama da mashawartan Sojoji na Amurka ke kokarin kwato birnin na Mosul da 'yan ta'ada na IS suka mamaye tun a cikin shekara 2014.