Daruruwan 'Yan Ta'addan Takfiriyyah Na ISIS Sun Halaka A Aleppo
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i9274-daruruwan_'yan_ta'addan_takfiriyyah_na_isis_sun_halaka_a_aleppo
Rahotanni daga kasar Syria na cewa daruruwan 'yan ta'addan Takfiriyyah Wahabiya ne suka rasa rayukansu a cikin gundumar Aleppo da ke kasar Syria, a ba ta kashin da aka yi da su a cikin makon nan.
(last modified 2018-08-22T06:58:43+00:00 )
Aug 07, 2016 00:56 UTC
  • Daruruwan 'Yan Ta'addan Takfiriyyah Na ISIS Sun Halaka A Aleppo

Rahotanni daga kasar Syria na cewa daruruwan 'yan ta'addan Takfiriyyah Wahabiya ne suka rasa rayukansu a cikin gundumar Aleppo da ke kasar Syria, a ba ta kashin da aka yi da su a cikin makon nan.

Tashar talabijin ta Almayadeen daga Aleppo ta bayar da rahoton cewa, a jiya an yi barin wuta mai tsanani tsakanin 'yan ta'addan na ISIS da kuma dakarun gwamnati, bayan da 'yan ta'addan suka kame wani bangare na kwalejin sojoji da ke kudancin birnin Aleppo, amma a jiya sojojin na Syria sun fitar da su baki daya daga kwalejin, bayan halaka adadi mai yawa daga cikinsu.

A nasu bangaren mayakan Kurdawa na Syria Democrat da Amurka ke mara ma baya, sun kori 'yan ta'addan na ISIS daga yankin Manbij da ke kudancin gundumar ta Aleppo baki daya.

Wata cibiya da ke da alaka da 'yan tawayen Syria da ke da mazauni London wadda ke kiran kanta cibiyar kare hakkin bil adama a Syria, ta sanar da cewa fiye da mutane 700 ne suka rasa rayukansu a artabun da aka yi tsakanin sojojin Syria da da mayakan ISIS a Aleppo, amma mafi yawansu mayakan kungiyar ta ISIS ne.