Syria : Akwai Bukatar Isar Da Kayan Agaji Cikin Gaggawa A Aleppo
MDD, ta ce tana da bukatar isar da agaji cikin gaggawa ga mazauna birnin Aleppo na kasar Syria dake cikin tsaka mai wuya a daidai lokacin da sojoji da 'yan tawayen kasar ke shirin shiga wani sabon fada.
Kimanin mutane miliyan daya da rabi ne ke iya shiga halin kakani-kayi a wannan yankin inji MDD mundin dai ba'a taimaka ba.
A wata sanarwa da suka fitar ranar Litinin, jagoran ayyukan jin kai na MDD a Syria, Yakub El Hillo da kuma takwaransa a yankin, Kevin Kennedy sun bukaci bangarorin biyu da a dakatar da yaki domin gudanar da ayyukan jin kai.
kungiyoyin na bukatar da a samar masu da wani lokaci na akalla sa'o'I 48 domin isar da kayan agaji da magunguna ga mabukata.
Rikicin Syria wanda ya barke tun a cikin shekara 2011 yayi sanadin mutuwar mutane 290,000 tare da cilastawa rabin al'umma kasar tserewa daga gidajensu.